IQNA

Za A Nuna Wani Mushafin Kur'ani Mai Tsarki Na Kasar Mauritaniya

12:13 - July 13, 2011
Lambar Labari: 2153910
Bangaren kasa da kasa, za a nuna wani mushafin kur'ani mai tsarki na kasar Mauritaniya da aka kira mushafin kasa mai suna Shakit, wanda za a kammala dukkanin ayyukansa daga nan zuwa karshen wannan shekara da muke ciki.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labar da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na ami an bayyana cewa, za a nuna wani mushafin kur'ani mai tsarki na kasar Mauritaniya da aka kira mushafin kasa mai suna Shakit, wanda za a kammala dukkanin ayyukansa daga nan zuwa karshen wannan shekara da muke ciki ta 2011.

Bayanin ya ci gaba da cewa an rubuta wannan kur'ani mai tsarki ne da salon rubutu na kasar d ake yin amfani da shi a hukumance, kuma a cikin wannan mako da muek ciki ne za a gyara bangare kashi uku bisa hudu na mushafin da aka kammala rubutunsa a birnin Nuwakshout fadar mulkin kasar.

Yanzu haka dai ana shirin nuna wani mushafin kur'ani mai tsarki na kasar Mauritaniya da aka kira mushafin kasa mai suna Shakit, wanda za a kammala dukkanin ayyukansa daga nan zuwa karshen wannan shekara da muke ciki kamar dai yadda ma'aikar kula da harkokin addini ta kasar ta sanar.

824520


captcha