IQNA

Birnin Najaf Zai Dauki Nauyin Gasar Kur’ani Ta Duniya A Cikin Shekara Ta 2012

14:45 - July 14, 2011
Lambar Labari: 2154484
Bangaren kasa da kasa, shugaban kwamitin makaranta da mahardata kur’ani mai tsarki na birnin Najaf mai alfarma ya bayyana cewa an fara gudanar da dukkanin shirin da ya kamata domin gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da za agudanar a birnin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, shugaban kwamitin makaranta da mahardata kur’ani mai tsarki na birnin Najaf mai alfarma ya bayyana cewa an fara gudanar da dukkanin shirin da ya kamata domin gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da za a gudanar a birnin a matsayi na duniya baki daya a cikin shekara ta 2012.
Shugaban kwamitin Sayyid Kasim Alhulwu ya bayyana cewa, wanna gasa za ta hada da bangarori daban-daban na karatu da hardar kur’ani mai tsarki, kamar yadda za ta shafi bangaren tafsiri da kuma dalilan safkar ayoyin kur’ani da abubuwan da suka danganci ayar, gami da kuma ilimin sanin ka’idojin karatu na tajwidi.
Shugaban kwamitin makaranta da mahardata kur’ani mai tsarki na birnin Najaf mai alfarma ya bayyana cewa an fara gudanar da dukkanin shirin da ya kamata domin gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da za a gudanar a birnin mai alfarma.
824804


captcha