IQNA

Kudurce Mai Tseratar Da Duniya Na Nuni Da Bukatar Wani Abun Koyi Ga Bil Adama

16:13 - July 16, 2011
Lambar Labari: 2155277
Bangaren kasa da kasa, kudurce wani mutum mai tseratar da bil adama a karshen duniya, wata lama ce da ke nuni da cewa dukkanin mutane sun yarda da cewa akwai wani abun koyi da mutane za su bi shi domin tabbatar da adalci a bayan kasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ya yi da wani daya daga cikin mahalarta taron mahdawiyya daga kasar Sweeden Hans Auko ya bayyana cewa, kudurce wani mutum mai tseratar da bil adama a karshen duniya, wata lama ce da ke nuni da cewa dukkanin mutane sun yarda da cewa akwai wani abun koyi da mutane za su bi shi domin tabbatar da adalci a bayan kasa tare da tseratar da bil adama.

Dokta Hans ya ce dukkanin mabiya addinai na muslunci da kiristanci da yahudanci sun amince kan cewa wani mutum zai bayyana daga karshen duniya bayan zalunci ya mamaye duniya, 'yan adam sun shiga dimuwa da fangima da dirkaniyya, kuma hakan ya tabattar da cewa imanisu kan wanna akida ya yi kusa matuka.

Kudurce wani mutum mai tseratar da bil adama a karshen duniya, wata lama ce da ke nuni da cewa dukkanin mutane sun yarda da cewa akwai wani abun koyi da mutane za su bi shi domin tabbatar da adalci a bayan kasa baki daya, tare da samar da yanayi na rayuwa mai kyau ga 'yan adam.

826245

captcha