Bangaren kasa da kasa, an tsaurara matakan tsaro a birnin Karbala mai alfarma a daidai lokacin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) suke ci gaba da isa birnin domin halartar tarukan tunawa da zagayowar ranar haihuwar Imam Mahdi (AS)
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadrawa na yanar gizo na alfayhaa cewa, an tsaurara matakan tsaro a birnin Karbala mai alfarma a daidai lokacin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) suke ci gaba da isa birnin domin halartar tarukan tunawa da zagayowar ranar haihuwar Imam Mahdi (AS) kamar yadda aka saba yi a kowace shekara.
Babban jami'in 'yan sanda na birnin Karbala mai alfarma Ahmad Zuwaini ya bayyana cewa, ya zuwa sun kammala daukar dukkanin matakan da suka dace domin bayar da kari ga masu gudanar da tarukan addini na tinawa da ranar haihuwar Imam Mahdi (AS) a birnin, wadanda suka fito daga sassa daban-daban na kasar da ma wasu kasashen ketare, domin halartar wadannan taruka masu albarka.
Ana ci gaba da tsaurara matakan tsaro a birnin Karbala mai alfarma a daidai lokacin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) suke ci gaba da isa birnin domin halartar tarukan tunawa da zagayowar ranar haihuwar Imam Mahdi (AS) a birnin mai alfarma.
825644