Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar Imam Hussain (AS) mai kula da shirya tarukan addini a birnin Karbala mai alfarma, za ta dauki nauyin shirya wani taron alkur'ani mai tsarki a birnin Dakar na kasar Senegal a cikin watan Ramadan mai zuwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nun an bayyana cewa, babbar cibiyar Imam Hussain (AS) mai kula da shirya tarukan addini a birnin Karbala mai alfarma, za ta dauki nauyin shirya wani taron alkur'ani mai tsarki a birnin Dakar na kasar Senegal a cikin watan Ramadan mai zuwa, wanda zai samu halartar daliban makarantu da cibiyoyin addini na kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa a bangare guda kuma babban jami'in 'yan sanda na birnin Karbala mai alfarma Ahmad Zuwaini ya bayyana cewa, ya zuwa sun kammala daukar dukkanin matakan da suka dace domin bayar da kari ga masu gudanar da tarukan addini na tinawa da ranar haihuwar Imam Mahdi (AS) a birnin, wadanda suka fito daga sassa daban-daban na kasar da ma wasu kasashen ketare, domin halartar wadannan taruka masu albarka.
Ana ci gaba da tsaurara matakan tsaro a birnin Karbala mai alfarma a daidai lokacin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) suke ci gaba da isa birnin domin halartar tarukan tunawa da zagayowar ranar haihuwar Imam Mahdi (AS) a birnin mai alfarma.
Babbar cibiyar Imam Hussain (AS) mai kula da shirya tarukan addini a birnin Karbala mai alfarma, za ta dauki nauyin shirya wani taron alkur'ani mai tsarki a birnin Dakar na kasar Senegal a cikin watan Ramadan mai zuwa na shekarar bana.
826168