IQNA

Babu Banbamci Mai Yawa Tsakanin Mazhabobin Musulunci Dangane Da Mahadi

16:09 - July 16, 2011
Lambar Labari: 2155283
Bangaren kasa da kasa, wani babban malamin falsafa a jam'ar Kontaki ta kasar Amurka ya bayyana cewa babu banbamci mai yawa tsakanin mahangar manyan mazhabobin muslunci byu dangane da Mahdi (AS) wato mazhabobin sunna da shi'a.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Alyour Liman wani babban malamin falsafa a jam'ar Kontaki ta kasar Amurka ya bayyana cewa babu banbamci mai yawa tsakanin mahangar manyan mazhabobin muslunci byu dangane da Mahdi wato mazhabobin sunna da shi'a, wadanda su ne mazhabobi mafi girma a cikin addinin muslunci.

A wata zantawa da ya yi da wani daya daga cikin mahalarta taron mahdawiyya daga kasar Sweeden Hans Auko ya bayyana cewa, kudurce wani mutum mai tseratar da bil adama a karshen duniya, wata lama ce da ke nuni da cewa dukkanin mutane sun yarda da cewa akwai wani abun koyi da mutane za su bi shi domin tabbatar da adalci a bayan kasa tare da tseratar da bil adama.

Ya ce dukkanin mabiya addinai na muslunci da kiristanci da yahudanci sun amince kan cewa wani mutum zai bayyana daga karshen duniya bayan zalunci ya mamaye duniya, 'yan adam sun shiga dimuwa da fangima da dirkaniyya, kuma hakan ya tabattar da cewa imanisu kan wanna akida ya yi kusa matuka.

Babban malamin falsafa a jam'ar Kontaki ta kasar Amurka ya bayyana cewa babu banbamci mai yawa tsakanin mahangar manyan mazhabobin muslunci byu dangane da Mahdi (AS) wato mazhabobin Musulunci da suka fi shahara a duniya.

826165


captcha