Bangaren kasa da kasa, an wani babban dakin cikin abinci mafi girma na halal a birnin Roubais na kasar Faransa, wanda yake gudanar da lamurraansa daidai da akida ta musulunci, wanda ya samu karbuwa daga mabiya addinin muslunci na kasar, musamman wadanda suke raywa a birnin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyan cewa, an wani babban dakin cikin abinci mafi girma na halal a birnin Roubais na kasar Faransa, wanda yake gudanar da lamurraansa daidai da akida ta musulunci, wanda ya samu karbuwa daga mabiya addinin muslunci na kasar, musamman wadanda suke raywa a birnin da suke halartar tarukan da ake gudanarwa na addinnin muslunci.
A labarin da ya nakalto kuma daga shafin yanar gizo na Bernama cewa, pira ministan kasar Malazia ya jaddada muhimmancin gudanar da tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya, a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban taron bude gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar ta Malazia.
Bayanin ya ci gaba da cewa a wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na lebanonfiles an bayyana cewa, fadar Vatican ta mabiya addinin kirista da ke birnin Rom na kasar Italia za ta shiya gudanar da wani zaman taro na tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya, wanda zai yi dubi kan muhimman batutuwa da suka hada dukkanin bangarorin ta yadda za a kara samun fahimtar juna tsakaninsu.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daga cikin ayyukan da fadar vatican ta saba shiryawa tun lokacin tsohon paparoma na biyu, wanda ya sa hakan ya zama wani zaman taro na shekara-shekara da ta saba gudanarwa, tare da halartar masana da malamai daga sassa daban-daban na kasashen duniya, da suka hada kasashen larabawa da na musulmi.
826139