Bangaren fikira da ilimi, an fara gudanar da taron bayar da horo ga malaman makarantu da suke koyar da harshen farisanci a kasar Lenanon wanda aka fara a birnin Beirut fadar mulkin kasar a karo na goma sha biyu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama’a na karamin ofishin jakadancin jamhuriyar muslunci ta Iran a Lebanon an bayyana cewa, an fara gudanar da taron bayar da horo ga malaman makarantu da suke koyar da harshen farisanci a kasar Lenanon wanda aka fara a birnin Beirut fadar mulkin kasar a karo na goma sha biyu da ake gudanarwa akasar.
Karamin ofishin jakadancin kasar Iran da ke birnin na Beirut shi ne ya dauki nauyin shiryawa da gudanar da wannan shiri kamar yadda ya saba yi a lokutan baya, da nufin kara karfafa dangantaka ta fuskacin yada al’adu tsakanin al’ummomin wadannan kasashe biyu masu kyakkyawar dangantaka tsakninsu a tsawon shekaru.
Yanzu haka dai an fara gudanar da taron bayar da horo ga malaman makarantu da suke koyar da harshen farisanci a kasar Lenanon wanda aka fara a birnin Beirut fadar mulkin kasar a karo na goma sha biyu a birnin na kasar ta Lebanon.
826556