Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, ana shirin gudanar da tarukan ranar sha biyar ga watan sha'aban domin tunawa da haihuwar Imam Zaman Al-mahdi (AS) a babbar cibiyar muslunci ta Imam Ali (AS) da ke birnin Veina na kasar Austria wanda zai samu halartar mabiya addinin muslunci na kasar.
Kakakin kungiyar tarayyar turai Jerzy Buzek, ya fadi jiya cewa ko alama ba za su amince da hukuncin kisan da kotun sojin kasar Bahrain ta yanke kan matasan hudu ba, kuma kungiyar tana yin kira ga mahukuntan kasar ta Bahrain ta kawo karshen yin amfani da karfin da take yi kan fararen hula masu neman a gudanar da sauye-sauyen siyasa.
A jiya ne wata kotun soji da mahukuntan Bahrain suka kafa cikin makwannin suka, ta yanke hukuncin kisa kan wasu matasa hudu, bisa zargin cewa suna da hannu wajen mutuwar 'yan sanda biyu a lokacin gudanar da zanga-zanga a birnin Manama.
Al'ummomin duniya da dama da suka hada da kungiyoyin kare hakkin bil adama, suna ci gaba da yin Alawadai da mahukuntan kasar Bahrain da kuma na Saudiyya, sakamakon yin amfani da karfin soji da suka yi wajen yin kisan gilla a kan fararen hula masu neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa ta hanyar lumamana a cikin kasar. 826350