IQNA

Babbar Kotun Kolin Kasar Birtaniya Ta Bayar Da Umurnin Sain Sheikh Ra'id Salah

18:10 - July 17, 2011
Lambar Labari: 2155441
Bangaren kasa da kasa, babbar kotun kolin kasar Birtaniya ta bayar umurnin sakin sheikh Ra'id Salah shugaban harkar Musulunci ta palastinu a cikin yankunan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta mamaye a cikin shekara ta 1948.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na palastine an bayyana cewa, babbar kotun kolin kasar Birtaniya ta bayar umurnin sakin sheikh Ra'id Salah shugaban harkar Musulunci ta palastinu a cikin yankunan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta mamaye a cikin shekarun baya.
Wannan mataki na kotun ta birnin London ya z one bayan da babban alkalinta ya saurari sheda dangane da kame sheikh Ra'id Salah da jami'an tsaron kasar suka yi a kwanakin baya, inda ya bayyana cewa babu wani dalili da ke nuni da cewa zuwansa yana tattare da barazana ga harkar tsaron kasar Birtaniya kamar yadda jami'an tsaron gwamnati suka sheda ma kotun.
A kan haka babbar kotun kolin kasar Birtaniya ta bayar umurnin sakin sheikh Ra'id Salah shugaban harkar Musulunci ta palastinu a cikin yankunan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta mamaye, kuma ranar Litinin mai zuwa ce zai fito daga kurkun da ake tsare da shi a birnin London.
826601

captcha