IQNA

Tsarin Musulunci Tsari Ne Da Yaginu Kan Akidar Bin Tafarkin Mahdawiyya

17:09 - July 18, 2011
Lambar Labari: 2155973
Bangaren siyasa da zamanatakewa, tsarin addinin muslunci tsari ne da ya ginu a kan koyarwa ta tafarkin mahdawiyya, bisa la’akari da cewa wannan zamani na shugabancin mahdi ne a kan haka dole ne duk wani tsarin muslunci da ke bin tafarki na manzon Allah ya zama bisa akida ta jiran Mahdi (AS)
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ya yi da babban daraktan jaridar Kaihan International ya bayyana cewa, tsarin addinin muslunci tsari ne da ya ginu a kan koyarwa ta tafarkin mahdawiyya, bisa la’akari da cewa wannan zamani na shugabancin mahdi ne a kan haka dole ne duk wani tsarin muslunci da ke bin tafarki na manzon Allah ya zama bisa akida ta jiran Mahdi (AS) domin kuwa shi ne imamin wannan al’umma ta manzon Allah ta karshen zamani.
Wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar sharq akl-ausat an bayyana cewa, ana shirin bude wani baje koli na kayan muslunci da suka hada littafai da kuma abubuwan da ke nuni da matsayin ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya.
A bangare guda kuma a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo Express Tribune an bayyana cewa, ana nuna wani dadden kwafin kur’ani mai tsarki a birnin Karachi na kasar Pakistan, wanda ya kunshi matani kur’ani na larabci da kuma tarjamar wasu bangarori a cikin harshen da ake magana da shi a kasar tsawon zamunna da suka gabata.
Wasu rahotannin kuma sun yi nuni da cewa mabiya addnin muslunci na kasar Italia musamman ma mazauna birnin Rom, suna ganin cewa bisa la’akari da yawan da suke da shi a kasar, daidai da ddokokin da aka amince da su auna da ahakkin su mallaki babban masallacin juma’a a cikin birnin Roma, kuma sun aike da takardun neman izini kan hakan, amma har yanzu mahukunta ba su ce komai ba kan wannan lamari.
826872
captcha