Bnagaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da wani zaman taro na bunkasa harkokin al'adun muslunci a kasar faransa, wanda babbar cibiyar kula da harkokin musulmi ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin watanni biyu masu zuwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqnaya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga wani shafin yanar gizo an bayyana cewa, ana shirin fara gudanar da wani zaman taro na bunkasa harkokin al'adun muslunci a kasar faransa, wanda babbar cibiyar kula da harkokin musulmi ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin watanni biyu masu zuwa wanda zai daiadai da watan Satumban wannan shekara.
Daga cikin jagororin gungun 'yan siyasar na Alwifaq Hadi Musawi ya bayyana cewa, sun dauki wannan matakin ne bayan da suka fahimci cewa tattaunawar ta yi kama da wasan kwakwayo, domin kuwa ana tattauna abin da sarki da gwamnatin kasar suke bukata ne, ba abin da al'ummar Bahrain ke bukata ba, domin kuwa a cewarsa sun shiga tattaunawar ne suna masu riko da sauye-sauyen da al'ummar kasar fatan gani a cikin harkokin siyasa da mulkin kasar.
Da dama daga cikin matasan kasar Bahrain da suke gudanar da zanga-zangar neman sauyi, sun yi Allawadai da wannan tattaunawa, wadda ake gudanarwa a lokacin mahukuntan kasar suke ci gaba da kame daruruwan masu zanga-zanga tare da azabtar da su, inda wasunsu sukan rasa rayukansu sakamakon azabtarwa.
827271