Bangaren kasa da kasa, cibiyar shirya gasar karatun kur'ani mai tsarki ta birnin Dubai cibiyar kasuwanci kasar hadaddiyar daular larabawa ta sanar da shirin gasar da za a gudanar a birnin a matsayi na kasa da kasa a cikin watan Ramadan mai alfarma da ke zuwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar darul khalij an bayyana cewa, cibiyar shirya gasar karatun kur'ani mai tsarki ta birnin Dubai cibiyar kasuwanci kasar hadaddiyar daular larabawa ta sanar da shirin gasar da za a gudanar a birnin a matsayi na kasa da kasa a cikin watan Ramadan mai alfarma da ke zuwa nan da kasa da makonni biyu.
Malamin ya ci gaba da cewa babbar manufar haramtacciyar kasar yahudawan sahyuniya ita ce ganin an samu rarrabuwar kawuna tsakanin mabiya addinin muslunci, wadanda suka hada sunna da shi'a kuma ta hanayar kawo rikici tsakanins za a iya haifar da baraka tsakanin muslumi, wanda kuma hakan na daga cikin ayyukan da Husni Mubarak ya daukar ma kansa yi.
Babban malamin jami'ar Azhar mai bayar da fatawa a lokacin da yake zantawa da wasu daga cikin 'yan siyasa da kuma ma'aikatan yada labarai na kasar Masar ya bayyana cewa, tsohon shugaban mulkin kama karya na Husni Mubarak shi ne ya kasance yana tuzura malaman kasar wajen kafirta mabiya mazhabar shi'a na kasar da ma na duniya baki daya.
827075