IQNA

A Cikin Watan Ramadan Za A Gudanar Tarukan Ramadan A Kasar Faransa

17:51 - July 20, 2011
Lambar Labari: 2157243
Bangaren kasa da kasa, a cikin watan ramadana mai alfarma za a gudanar da tarukan dararen qadr a masallatai da cibiyoyin addini na kasar Faransa kamar yadda aka saba yi a kowace shekara tare da halartar malamai da kuma shugabannin cibiyoyi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo sudoest an bayyana cewa, a cikin watan ramadana mai alfarma za a gudanar da tarukan dararen qadr a masallatai da cibiyoyin addini na kasar Faransa kamar yadda aka saba yi a kowace shekara tare da halartar malamai da kuma shugabannin cibiyoyin kasar.
a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na middle East Monitor cewa, ana shirin bude hanyoyin karkashin kasa da yahudawan sahyuniya suka gina karkashin masallacin Qods mai alfarma, a lokacin da al’ummomin duniya gami da shugabannin larabawa suka yi gum da bakinsu kan wannan tabargaza ta yahudawan sahyuniya a wurare masu tsarki na al’ummar musulmi.
Tun bayan da yahudawan sahyuniya suka fara gudanr da wannan aiki, masu ‘yancin siyasa daga cikin kasashen musulmi da kuma ‘yan kadan daga cikin kasashen larabawa, sun nuna rashin amincewarsu da wannan mummanan aiki da ke samun cikakken goyon baya daga gwamnatocin Amurka da munafukan larabawa, musamman ma wadanda suke da dangantaka ta zahiri da haramtacciyar kasar Isra’ila, da kuma masu dangantaka ta boye.
Ana shirin bude hanyoyin karkashin kasa da yahudawan sahyuniya suka gina karkashin masallacin Qods mai alfarma, a lokacin da al’ummomin duniya gami da shugabannin larabawa suka yi gum da bakinsu kan wannan tabargaza ta yahudawan sahyuniya.
827816

captcha