IQNA

Za A Gudanar Da Wani Zaman Horo Na Samun Masani Kan Ilmomin Ahlul Bait

17:50 - July 20, 2011
Lambar Labari: 2157245
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da wani zaman taro na bayar da horo kan ilmomin ahlul bait a cibiyar jamiyar markazin ahlul bait da ke birnin Sikaso na kasar Mali, wanda za afara daga farkon makon gobe tare da halartar masana daga jami’oin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, ana shirin fara gudanar da wani zaman taro na bayar da horo kan ilmomin ahlul bait a cibiyar jamiyar markazin ahlul bait da ke birnin Sikaso na kasar Mali, wanda za afara daga farkon makon gobe tare da halartar masana daga jami’oin kasar da kuma cibiyoyin addini.
Rahoto ya ci gaba da cewa a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar the News an bayyana cewa, shugaban cibiyar jami’at Islami na kasar pakistan ya kirayi dukkanin malaman addinin muslunci da kuma masana, da su ajiye duk banbancin fahimta a gefe, su hada kai domin tunkarar makircin da ake kulla wa addinin muslunci, inda ya ce wanmnan wajibi ne da ya rataya kansu baki daya ba tare da fitar da wani bangare ba.
A banagare guda kuma an gudanar dawani zaman taro a kasar Birtaniya na mabiya addnin muslunci, a yayin gudanar da zama masana da malaman jami’oi za su halarta kuma za su gabatar da laccoci ga mahalrta taron, daga cikin muhimman abubuwan da taron zai mayar da hankali kansu akwai nazari kan matsayin sharia a cikin addinin muslunci, da kuma yadda wannan addini mai tsarki yake kallon rayuwar zamantakewa ta jama’a. 827668

captcha