Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, an nada sabon shugaban majalisar malaman addini na kasar Ivory Coast da nufin tabbatar da sabbin shirye-shiryenta wanda ya yi daidai da abin da sauran muslmin kasar suka amince da shi baki daya kamar yadda yadda majlaisar ta bayar da sanarwa.
Rahoton ya tabbatar da cewa a cikin wata mai kamawa ne za a gudanar da wani zama na karawa juna sani kan nazarin addinin musulunci, wanda za a gudanar a babban dakin gudanar da taruka na jami’ar Lise da ke kasar Birtaniya a karon farko.
babban malamin addnin muslunci a kasar Bahrain Ayatollah Isa Ahmad Kasim ya bayyana cewa, rusa masallatai mahukuntan kasar Bahrain da kuma na Saudiyya suke yi a acikin kasar Bahrain babban cin zarafi ne da keta alfarmar addinin muslunci, shehin malamain ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar hudubar juma’a abirnin Manama.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alalam an bayyana cewa, babban sakataren kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Bahrain Nabil Rajab ya bayyana cewa, gidan sarautar kasar ta Bahrain na kokarin tayar da fitinar mazhaba a cikin kasar, da nufin kawar da hankulan al’ummomin duniya kan barnar da suke tafkawa a cikin kasar, suna yin hakan ne kuwa ta hanyar rusa masallatai da wuraren tarukan addini na mabiya mazhabar iyaln gidan manzon Allah masu rinjaye a kasar.
827639