IQNA

Turkiya Da Kafkaz Suna Gudanar Da Ayyukan Hadin Hadin Gwiwa Na Addini

20:14 - July 21, 2011
Lambar Labari: 2157576
Bangaren siyasa da zamantakewa, kasar Turkiya tareda sauran al'ummomin yankin kafkaz suna gudanar da ayyuka na hadin gwiwa da nufin kara bunkasa bunkasa harkokin addini a tsakaninsu da ma yankin baki daya.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na islamsng an bayyana cewa, Turkiya tareda sauran al'ummomin yankin kafkaz suna gudanar da ayyuka na hadin gwiwa da nufin kara bunkasa bunkasa harkokin addini a tsakaninsu da ma yankin baki daya kasantuwar yankin mai yawan mabiya addinin muslunci.

Rahotanni daga kasar Syria sun habarta cewa kura ta lafa a garin Hums bayan dauki ba dadi da aka yi tsakanin masu zanga-zanga da wasunsu ke dauke da makamai, da kuma jami'an tsaro a daya bangaren.

Rahotannin sun nuna cewa rikicin na Hums ya yi sanadiyar mutuwar jami'an tsaro da kuma wasu daga cikin masu zanga-zanga, sakamakon musayar wutar da aka yi tsakanin bangarorin biyu, wadanda suka gani da idanunsu sun bayyana cewa an samu tarin makamai a wasu wurare a cikin birnin na Hums, an kuma kame mutane da dama da suke da hannu a tashetashen hankulan. A bangare guda kuma dubban daruruwan mutane sun gudanar da jerin gwano a birane daban-daban na kasar Syria, inda suke nuna goyon bayan ga shugaba Asad.

A nasa bangaren Ministan harkokin wajen kasar Syria Walid Mu'allim ya kashed ga Amurka da faransa, kan shigar shigular da suke yi a cikin harkokin Syria, inda ya sheda cewa jakadun kasashen biyu bas u da ikon fitadaga birnin Damascus zuwa wasu sassa na kasar said a izinin ma'aikatarsa. 828477
captcha