Bangaren kasa da kasa, wajibi ne da ya rataya kan mabiya addinin muslunci su karfafa hadin kan da ke tsakaninsu ta hanyar yin riko da koyarwar kur'ani mai tsarki a cikin dukkanin harkokinsu na rayuwar yau da kullum, kamar yadda kur'ani mai tsarki ya koyar da su.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na Bernama an bayyana cewa, mataimakin Piran ministan kasar Malazia ya ya yi kira da cewa wajibi ne da ya rataya kan mabiya addinin muslunci su karfafa hadin kan da ke tsakaninsu ta hanyar yin riko da koyarwar kur'ani mai tsarki a cikin dukkanin harkokinsu na rayuwar yau da kullum, kamar yadda kur'ani mai tsarki ya koyar da su, kuma muka gani a aikace a cikin sirar ma'iki.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bude wani babban taro na mabiya addinin musulunci a kasar a dakin taruka na birnin Kualalampour fadar mulkin kasar, inda ake tattaunawa kan muhimamn batutuwa da suke ci ma mabiya addinin muslunci tuwo a kwarya a cikin harkokin rayuwarsu ta yau da kullum, tare da duba hanyoyin magance matsalolinsu.
Mataimakin Pira ministan Malazia ya bayyana cewa wajibi ne da ya rataya kan mabiya addinin muslunci su karfafa hadin kan da ke tsakaninsu ta hanyar yin riko da koyarwar kur'ani mai tsarki a cikin dukkanin harkokinsu na rayuwar yau da kullum, kamar yadda kur'ani mai tsarki ya koyar da su a tsawon tarihi.
829398