Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taro kro na uku dangane da kur'ani mai tsarki a kasar Malazia, tare da halartar makaranta kur'ani mai tsarki daga kasashen duniya, da suka hada da na musulmi da kuma larabawa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, za a gudanar da taro kro na uku dangane da kur'ani mai tsarki a kasar Malazia, tare da halartar makaranta kur'ani mai tsarki daga kasashen duniya, da suka hada da na musulmi da kuma larabawa, domin halartar taron kamar yadda aka saba gudanar da shi a kowace shekara.
Dubban mutane suka gudanar da zanga-zanga a jiya a wasu birane na kasar Malawi, inda suke neman shugaban kasar Bingu Wa Mutharika ya safka daga kan mukaminsa bisa zarginsa da tauye 'yancin al'ummar kasa da cutar da tattalin arzikinta.
Rahotanni daga birnin Lilongwe fadar mulkin kasar Malawi sun habarta cewa, daruruwan masu zanga-zanga a ckin birnin sun kone motoci da ofisoshi gami da wuraren kasuwanci, da suka da dangantaka da wasu daga cikin ministoci da 'yan siyasa da suka fito daga jam'iya mai mulki a kasar, a birnin Blantyre ma cibiyar kasuwancin kasar da ma wasu garuruwan na daban an gudanar da irin wannan zanga-zanga, inda jami'an tsaro a cikin kayan sarki suka yi ta antaya hayaki mai sanya hawaye, tare da yin awon gaba da mutane da dama.
Masu zanga-zangar dai suna zargin shugaba Mutharika tare da mukarrabansa da yin watanda da dukiyar kasa, tare da gurgunta harkokin tattalin arzkin kasar.
829376