Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na islamonline an bayyana cewa, wata majiya ajami'ar Azhar da ke birnin alkahira na kasar Masar ta sanar cewa tana da shirin kafa wasu cibiyoyin addini a cikin yankunan Sudan ta kudu, da nufin kara kyautata dangantaka tsakanin al'ummar yankin da sauran kasashen musulmi da na larabawa.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na masrwy an bayyana cewa, jami'ar Azhar ta kasar Masar ta aike da wata wasika ta gargadi ga tashar talabijin ta Nile sat a shirin da take da shi na watsa wani fim na Imamai Hassan da Hussain a cikin watan Ramadan mai zuwa, saboda nuna fusakunsu da aka yi a cikin fim din, wanda jami'ar take ganin cewa hakan ya sabawa koyarwar muslunci a nuna fusakun ahlul bait masu tsarki a cikin fina-finai.
Jami'ar Azhar dai ita ce jami'ar musulucni mafi girma da jimawa awannan zamani, kuma bangarori daban-daban da suke kula da lamurran fatawa da sa ido kan abubuwan da ake aikatawa da matsayinsu a cikin addnin muslunci, musamman ma abubuwan da suka danganci muslunci da musulmi.
Dangane da hakan jami'ar Azhar ta kasar Masar ta aike da wata wasika ta gargadi ga tashar talabijin ta Nile sat a shirin da take da shi na watsa wani fim na Imamai Hassan da Hussain a cikin watan Ramadan mai zuwa, saboda nuna fusakunsu da aka yi a cikin fim din wanda shi ne karon farko da za awatsa shi.
Rahoton ya ci gaba da cewa wata majiya ajami'ar Azhar da ke birnin alkahira na kasar Masar ta sanar cewa tana da shirin kafa wasu cibiyoyin addini a cikin yankunan Sudan ta kudu, da nufin kara kyautata dangantaka tsakanin al'ummar yankin da sauran kasashen musulmi da na yankin baki daya.
829930