IQNA

An Gano Wani Makirci Kan Kafa Wani Gungun 'Yan Ta'adda A Bahrain

14:47 - July 24, 2011
Lambar Labari: 2159019
Bangaren kasa da kasa, an gano wani gagarumin makirci da pira ministan kasar Bahrain tare da hadin baki da babban mataimakin ministan harkokin cikin gidan kasar, kan kafa wani gungun 'yan ta'adda da masarautar kasar za ta dauki nauyinsu domin kisan gilla a kan manyan jagororin mazhabar shi'a akasar.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an gano wani gagarumin makirci da pira ministan kasar Bahrain tare da hadin baki da babban mataimakin ministan harkokin cikin gidan kasar, kan kafa wani gungun 'yan ta'adda da masarautar kasar za ta dauki nauyinsu domin kisan gilla a kan manyan jagororin mazhabar shi'a a kasar a wani sabon mataki na yunkurin ganin bayans, duk kuwa da cewa su ne masu rnjaye a kasar.

Pira ministan kasar ta Bahrain tare da surukinsa wanda shi ne mataimakin ministan harkokin cikin gida na kasar, sun hada baki wajen ganin sun aiwatar da wannan baker manufa, wanda ko shakka babu hakan ne zai kai ga kawo wani gagarumin canji a cikin kasar kamar dai yadda masana suke hasashe.

An gano wani gagarumin makirci da pira ministan kasar Bahrain tare da hadin baki da babban mataimakin ministan harkokin cikin gidan kasar, kan kafa wani gungun 'yan ta'adda da masarautar kasar za ta dauki nauyinsu domin kisan gilla a kan manyan jagororin mazhabar shi'a akasar ta Bahrain.

Mahukuntan kasar Bahrain dais un yi amfani da hanyoyi wajen murkushe zanga-zangar da mabiya tafarkin ahlul bait suke gudanarwa a kasar domin neman sauyi na siyasa, kamar dai yadda dukkanin dokokin kasa da kasa suka baiwa alummomi damar yin hakan.
829805
captcha