IQNA

Kungiyar Hadin Kan kasashen Musulmi Ta Yi Allawadai Da Harin Norway

9:29 - July 25, 2011
Lambar Labari: 2159321
Bangaren kasa da kasa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da kai harin kasar Norway, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 92, wasu da dama kuma suka samu munan raunuka, lamarin ya fuskanci suka.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto dag shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alhayat da ake bugawa a kasar saudiyya, an bayyana cewa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da kai harin kasar Norway, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 92, wasu da dama kuma suka samu munan raunuka, lamarin ya fuskanci suka da yin Allawadai daga kasashen duniya, da sauran kungiyoyi na kasa da kasa.

Lauyan mutumin nan da ake zargi da kai mummunan harin ta'addancin da aka kai kasar Norway a jiya ya bayyana cewar mutumin da ake zargin mai suna Anders Behring Brevik ya amince da cewa shi ne ya kai wannan hari da ya yi sanadiyyar mutuwar alal akalla mutane 92 da raunana wasu da dama.
Mr. Geir Lippestad lauyan mutumin da ake zargin ya shaidawa gidan talabijin din NRK na kasar Norway din cewa wanda ake zargin ya amince da aikata wannan danyen aikin, yana mai cewa duk da cewa abin da ya aikata din mummunan abu ne amma dai ya zama wajibi ya aikata hakan. Har ila yau lauyan ya kara da cewa tun a shekara ta 2009 ya ke shirya kai wannan harin.
Wasu bayanai da aka watsa a shafin internet suna nuni da cewa shi dai wannan mutumin yana da rikau ne da kuma kiyayya ga musulmi kamar yadda bayanai suke ci gaba da fitowa dangane da irin shirin da ya yi na kai wannan harin.
Yan sanda dai sun ce nan gaba kadan za a gurfanar da wannan mutumin a gaban kotu da zargin da ayyukan ta'addanci guda biyu. Na farko dangane da mutuwar mutane bakwai sakamakon tashin tashin bomb a garin Oslo, na biyu kuma dangane da kashe mutane sama da tamanin da biyar da ake zargin ya bindige su a wani sansanin matasa, kusa da birnin Oslon.
830296
captcha