Bangaren fikira da ilimi, karamin ofishin jakadancin jamhuriyar musulunci da ke birnin Bankuk na kasar Thailand ya hada wasu taron makaloli kan mahangar malamn addinin muslunci daga farabi har zuwa marigayi Imam Khomeini (RA)
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyan cewa, karamin ofishin jakadancin jamhuriyar musulunci da ke birnin Bankuk na kasar Thailand ya hada wasu taron makaloli kan mahangar malamn addinin muslunci daga farabi har zuwa marigayi Imam Khomeini, wadanda dukakninsu sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen tunani na addinin muslunci a duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa an harhada wadanan maklolin ne kuma aka tarjama su a cikin harshen Thailand, domin amfanin mutanen kasar da ma wadanda suke fahimtar harshen, duk kuwa da cewa hakan bay a nufin cewa a nan gaba ba za a tarjama su zuwa wasu yarukan duniya na daban ba, domin amfanin sauran al'ummomi.
Karamin ofishin jakadancin jamhuriyar musulunci da ke birnin Bankuk na kasar Thailand ya hada wasu taron makaloli kan mahangar malamn addinin muslunci daga farabi har zuwa marigayi Imam Khomeini, da nufin kara yada fikira ta addinin muslunci a kasar ta Thailand.
830402