IQNA

Shirin Bayar Da Horo Kan Harkokin Tattalin Arzikin Musulunci A Birnin London

16:14 - July 25, 2011
Lambar Labari: 2159421
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani shiri na bayar da horo kan harkokin kasuwanci a cikin addinin muslunci a birnin London fadar mukin kasar Birtaniya, wanda daya daga cikin fitattun jami'oin birnin za ta dauki nauyin shirayawa da gudanarwa.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na financeislamquefrance an bayyana cewa, an ji daga wani jami'in ilimi na kasar Birniya yana fadar cewa za a gudanar da wani shiri na bayar da horo kan harkokin kasuwanci a cikin addinin muslunci a birnin London fadar mukin kasar Birtaniya, wanda daya daga cikin fitattun jami'oin birnin za ta dauki nauyin shirayawa da gudanarwa a na gaba, duk kuwa da cewa ba a kayyade lokaci gudanarwa ba.
Wani rahoton kuma yana cewa dubban mutane suka gudanar da zanga-zanga a jiya a wasu birane na kasar Malawi, inda suke neman shugaban kasar Bingu Wa Mutharika ya safka daga kan mukaminsa bisa zarginsa da tauye 'yancin al'ummar kasa da cutar da tattalin arzikinta.

Rahotanni daga birnin Lilongwe fadar mulkin kasar Malawi sun habarta cewa, daruruwan masu zanga-zanga a ckin birnin sun kone motoci da ofisoshi gami da wuraren kasuwanci, da suka da dangantaka da wasu daga cikin ministoci da 'yan siyasa da suka fito daga jam'iya mai mulki a kasar, a birnin Blantyre ma cibiyar kasuwancin kasar da ma wasu garuruwan na daban an gudanar da irin wannan zanga-zanga, inda jami'an tsaro a cikin kayan sarki suka yi ta antaya hayaki mai sanya hawaye, tare da yin awon gaba da mutane da dama.

Masu zanga-zangar dai suna zargin shugaba Mutharika tare da mukarrabansa da yin watanda da dukiyar kasa, tare da gurgunta harkokin tattalin arzkin kasar. 830342
captcha