Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da taron kayan abincin halal a kasar China tare da halartar wasu daga cikin kamfanonin kasar da kuam wasu na kasashen gabacin Asia, musamman ma Malzia da Indonesia, inda ake nuna kaya daban-daban.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahot daga shafin sadarwa na aynar gizo na halal focus cewa, an fara gudanar da taron kayan abincin halal a kasar China tare da halartar wasu daga cikin kamfanonin kasar da kuam wasu na kasashen gabacin Asia, musamman ma Malzia da Indonesia, inda ake nuna kaya daban-daban da suke halal a cikin addinin muslunci, taron day a samu karbuwa daga mutanen kasar China musulmi da wadanda ba musilmi ba.
Daga lokacin da Ali Abdallah Saleh ya tafi kasar Saudiya, babban bukatar masu juyin juya halin kasar Yaman dai shi ne kafa kwamitin wucin gadi don gudanar da shugabanci da kuma kawar da jigajigan gwamnatin shugaba Saleh domin bude sabon shafi a siyasar kasar. Da yake gwamnatin Amurka tana kallon sauye sauyen da suke faruwa a Yaman da sauran kasashen Larabawa a matsayin barazana ga manufofinta da na HKI, tana bin hanyoyi daban daban cikinsu har da neman taimakon gwamnatin Saudiya domin hana alummar Yaman din cimma wannan buri na su.
Saboda haka ne masu samun goyon bayan Amurka a kasar ta Yaman a kullum suke bada labarin cewa Ali Abdallah Saleh ya kusan komawa gida, domin su kashe guiwar masu juyin juya hali. Ta wata fuskar kuma fadar White House tana tura manzanninta zuwa birnin San'aa domin neman mutanen da zasu iya maye gurbin Ali Abdallah Saleh wadanda kuma zasu kare manufofin Amurka.
Gudanar da taron kayan abincin halal a kasar China tare da halartar wasu daga cikin kamfanonin kasar da kuam wasu na kasashen gabacin Asia, musamman ma Malzia da Indonesia, inda ake nuna kaya, na da matukar muhimamnci ga musulmin kasar ta China.
830523