IQNA

Kasar Morocco Za Ta Dauki nauyin Taro Kan Tarjama Da Balagar Kur'ani

15:06 - July 26, 2011
Lambar Labari: 2160393
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa a Morocco kan tarjamar kur'ani mai tsarki zuwa harzunan duniya, atre da fitar da balaga wato zabar hikima da ke cikin kur'ani mai tsarki, wanda hakan zai bada dama a kara yada koyarwarsa a cikin duniya.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa a Morocco kan tarjamar kur'ani mai tsarki zuwa harzunan duniya, tare da fitar da balaga wato zabar hikima da ke cikin kur'ani mai tsarki, wanda hakan zai bada dama a kara yada koyarwarsa a cikin duniya domin amfanin mutane daban-daban a cikin harsunansu.

A wani labarin kuma, kasar Iran a shirye take ta sayarwa kasashe makobtanta da ma kadashen turai iskar gas.
Mohammad Ali-Abadi ministan riko na man fetur ne ya bayyana haka a jiya litinin, a wani bukin rattaba hannun kan yerjejeniyar shimfida bututun gas a kudancin kasar, bututu wanda zai ratsa kasashen Iraqi da kuma Syria zuwa kasashen turai.
A halin yanzu dai kasar Iran tana samarda cubic mita miliyon 600 na iskar gas a ko wace rana, sannan tana sayarda cubic Mita miliyon 37 daga ciki.
Ali-Abida ya ce idon an kammala aikin shimfida bututun, kasar Syria zata yi amfani da cubic mita miliyon 20-25 ko wace rana, hakama kasar Iraqi zata amfana da iskar gas din.
A bukin wanda a aka gudanar kudancin kasar Iran, kasashen Iraqi da syria sun amince da shimfida bututun wanda zai ratsa kasashen biyu zuwa kasar Lebanon daga nan kuma zuwa wasu kasashen Turai. 831237
captcha