Bangaren kasa da kasa, babban malamin jami'ar Azhar kuma mai bayar da fatawa a jami'ar da ke can kasar Masar Ahmad Tayyib ya bayyana cewa, wajibi ne musulmi da suka hada da sunan da shi'a su rika gudanar da ayyuka na bai daya domin ci gaban addinin musluncia duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yanar gizo na jaridar yaum sabi da aka ebugawa akasar maser ya bayyana cewa, babban malamin jami'ar Azhar kuma mai bayar da fatawa a jami'ar da ke can kasar Masar Ahmad Tayyib ya bayyana cewa, wajibi ne musulmi da suka hada da sunan da shi'a su rika gudanar da ayyuka na bai daya domin ci gaban addinin musluncia duniya da kuma samun hadin kai a tsakninsu mai dorewa.
jami'ar Azhar ta kasar Masar ta aike da wata wasika ta gargadi ga tashar talabijin ta Nile sat a shirin da take da shi na watsa wani fim na Imamai Hassan da Hussain a cikin watan Ramadan mai zuwa, saboda nuna fusakunsu da aka yi a cikin fim din, wanda jami'ar take ganin cewa hakan ya sabawa koyarwar muslunci a nuna fusakun ahlul bait masu tsarki a cikin fina-finai.
Wannan jami'ar ta Azhar dai ita ce jami'ar musulucni mafi girma da jimawa awannan zamani, kuma bangarori daban-daban da suke kula da lamurran fatawa da sa ido kan abubuwan da ake aikatawa da matsayinsu a cikin addnin muslunci, musamman ma abubuwan da suka danganci muslunci da musulmi.
Dr. Ahmad Tayyib babban malamin jami'ar Azhar kuma mai bayar da fatawa a jami'ar da ke can kasar Masar ya bayyana cewa, wajibi ne musulmi da suka hada da sunan da shi'a su rika gudanar da ayyuka na bai daya domin ci gaban addinin muslunci.
832005