Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na islamemfrance an bayyana cewa, a karon farko an bude wani wurin sayar da kayan wayar tarho ta tafi da gidanka akasar faransa wanda mabiya addinin muslunci suka bude a kasar tare da amincewar mahukuntan kasar domin samun damar sayen abubuwan da suke bukata daga hannun 'yan uwansu musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa an bude wannan wuri a lokacin da ake shirin fara azumin watan Ramadan mai alfarma, inda miliyoyin musulmi da suke rayuwa akasar suke cikin shirin fara ibadar wannan wata mai alfarma da albarka daga gobe litinin idan Allah mai kowa da komai ya kai mu.
A karon farko an bude wani wurin sayar da kayan wayar tarho ta tafi da gidanka akasar faransa wanda mabiya addinin muslunci suka bude a kasar tare d amincewar mahukunta kamar dai yadda majiyar babbar cibiyar kula da ayyukan muslunci ta kasar ta bayar da sanarwa.
833614