Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na tashar sadarwa ta rasid an bayyana cewa, da dama daga cikin kasashen musulmi da na larabawa sun fara azumi daga yau ranar litinin bayan da hukumominsu suka tabbatar da ganin watan Ramadan mai alfarma inda suka sanar a hukumance kan daukar azumin tare da fara gudanar da dukkanin abubuwan da ake yi a cikin wannan wata mai tsarki.
Bayanin ya ci gaba da cewa, a kasar Saudiyya ofishin sarkin kasar bangaren kula da harkokin addini ya fitar da sanarwar da ke cewa, duk da cewa ba a ga watan a cikin sararin samaniya ba, amma ranar lahadi ita ce rana ta karashe a wata sha'aban, wanda hakan ke tabbatar da fara watan watan Ramadan daga daren litinin, inda aka tashi da azumi a yau.
Da dama daga cikin kasashen musulmi da na larabawa sun fara azumi daga yau ranar litinin bayan da hukumominsu suka tabbatar da ganin watan Ramadan mai alfarma inda suka sanar a hukumance kan daukar azumin watan na Ramadan kamar dai yadda aka saba a kowace shekara.
834466