IQNA

An Girmama Wadanda Suka Gudanar Da Gasar Hardar Kur'ani A Kasar Niger

14:17 - August 01, 2011
Lambar Labari: 2163413
Bangaren kasa da kasa, an girmama wadanda suka gudanar da gasar harder kur'ani mai tsarki ta Almahir a jamhuriyar Niger wadda ta samu halartar makaranta da mahardata daga sassa daban-daba na kasar.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Riyad da ake bugawa a kasar saudiyya an bayyana cewa, an girmama wadanda suka gudanar da gasar harder kur'ani mai tsarki ta Almahir a jamhuriyar Niger wadda ta samu halartar makaranta da mahardata daga sassa daban-daba na kasar kamar dai yadda rahoton ya tabbatar.

Bayanin ya ci gaba da cewa babbar cibiyar yada al'adu ta Amir Sultan da ke kasar saudiyya ce tare da hadin gwiwa da ma'aikatar kula da harkokin addini ta jamhuriyar ce ta dauki nauyin shirya wannan gasar harder kur'ani, wadda ta samu halartar dalibai akalla 55 daga sassan kasar.

Girmama wadanda suka gudanar da gasar harder kur'ani mai tsarki ta Almahir a jamhuriyar Niger wadda ta samu halartar makaranta da mahardata daga sassa daban-daba na kasar zai kara karfafa gwiwar sauran makaranta da mahardata na kasar wajen shiga cikin irin wannan gasa.

834392


captcha