IQNA

15:40 - August 02, 2011
Lambar Labari: 2164116

Kasar Morocco Ta Sanar Da Ranar Talata ranar Farko Ta Watan Ramadan

Bangaren kasa da kasa, ma'aikatar harkokin addini ta kasar Morocco ta sanar cewa ranar talata it ace ranar farko watan ramdan a kasar, wadda za a tashi da azumi a cikinta a kasar baki daya a hukumance kamar yadda kwamitin ganin wata na ma'aikatar ya sanar jiya.




Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na emarrakech an bayyana cewa, ma'aikatar harkokin addini ta kasar Morocco ta sanar cewa ranar talata it ace ranar farko watan ramdan a kasar, wadda za a tashi da azumi a cikinta a kasar baki daya a hukumance kamar yadda kwamitin ganin wata na ma'aikatar ya sanar jiya bayan duba wata ranar da ta gbata a kasar ba a gan shi ba.

Wani labari day a nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na Benama an bayyana cewa, a dare na bakwai a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta duniya da ake gudanarwa a birnin Kualalmpour na kasar Malazia, makaranta bakwai ne suk kara da juna da suka kunshi maza biyar da kumamata biyu a gasar da ake gudanarwa a karo na hamsin da uku.

Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin wadanda suka kai ga wannan mataki hard a 'yan kasashen Sudan, Viatnam, Thailand, Senegal, Srilanka da dai sauransu, lamarin day a bayar da matukar mamaki, domin babu ko daya daga cikin kasashen da ta samu kaiwa zuwa ga mataki na karshe a gasar.

A dare na bakwai a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta duniya da ake gudanarwa a birnin Kualalmpour na kasar Malazia, makaranta bakwai ne suk kara da juna da suka kunshi maza biyar da kumamata biyu domin neman kaiwa ga mataki na karshe a wanna gasa.
834877
captcha