Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an bude wani babban dakin karatun littafan addinin muslunci ta hanyar yanar gizo a kasar Burnei, tare da saka littafai da mabiya addinin muslunci suke da bukata da su a cikin wannan zamani da muke wanda ake yin amfani da hanyar sadarwa ta yanar gizo fiye da duk wani lokacin da ya gabata.
Kasar dai tan taka gagarumar rawa ta fuskacin raya ayyuka na kur'ani da suka hada da shiriya tarukan addini da suke yin bahasi kan kur'ani da ilmomonsa, gami da irin wannan gasa da teke daukar nauyin shiryawa a kowace shekara bude wani babban dakin karatun littafan addinin muslunci ta hanyar yanar gizo a kasar Burnei, tare da saka littafai da mabiya addinin muslunci suke da bukata da su a cikin wannan zamani.
Rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na islamonline an bayyana cewa, wata majiya ajami'ar Azhar da ke birnin alkahira na kasar Masar ta sanar cewa tana da shirin kafa wasu cibiyoyin addini a cikin yankunan Sudan ta kudu, da nufin kara kyautata dangantaka tsakanin al'ummar yankin da sauran kasashen musulmi.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na masrwy an bayyana cewa, jami'ar Azhar ta kasar Masar ta aike da wata wasika ta gargadi ga tashar talabijin ta Nile sat a shirin da take da shi na watsa wani fim na Imamai Hassan da Hussain a cikin watan Ramadan mai zuwa, saboda nuna fusakunsu da aka yi a cikin fim din, wanda jami'ar take ganin cewa hakan ya sabawa koyarwar muslunci a nuna fusakun ahlul bait masu tsarki.
834855