Bangaren kasa da kasa, a yau ne ake gudanar da zaman kotun tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar Husni Mubarak, tare da 'ya'yansa biyu da kuma wasu daga cikin mukarrabansa bisa zarginsu da tafka data'asa da dukiyoyin jama'a.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wanilabari day a nakalto daga wata kafar sadarwa an bayyana cewa, a yau ne ake gudanar da zaman kotun tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar Husni Mubarak, tare da 'ya'yansa biyu da kuma wasu daga cikin mukarrabansa bisa zarginsu da tafka data'asa da dukiyoyin jama'a da kuma yin kisan gilla kan masu gudanar da zanga-zanga a kasar.
Rahotonni suna bayyana cewa: tsohon shugaban kasar Masar Husni Mubarak ya shiga cikin mummunan yana yi da tashin hankali tun bayan sanar da shi cewa zai gurfana a gaban kotu a ranar laraba.
Kafar Internet ta Arrisala-Net ta habarta cewa: Wata majiya mai tushe a asibitin garin Sharmus-Sheikh na kasar Masar ta bayyana cewa: tun daga lokacin da aka sanar da Husni Mubarak cewa a ranar laraba zai gurfana a gaban kotu kan laifuka da ake zarginsa da aikata su, yana yin jikinsa ya tabarbare tare da shiga cikin tsananin tashin hankali da kaduwa da za a iya gani a fuskarsa.
A gobe laraba ne ake sa ran kotun da ke shari'ar manyan laifuka a birnin Alkahira zata fara gudanar da shari'ar tsohon shugaban kama karya na kasar Masar Husni Mubarak, to sai dai ga dukkan alamu mummunan halin da ya shiga ba zai yi yuwa ya gurfana a gaban kotun ba.
836599