Bangaren al'adu da fasaha, an bude wani babban baje koli na kayayyakin rubuce-rubucen Iraniyawa da suke da dangantaka da addinin muslunci a kasar malazia tare da wasu daga cikin littafn da aka tarjama daga harshen farisanci zuwa harshen Malayu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NN an bayyana cewa, an bude wani babban baje koli na kayayyakin rubuce-rubucen Iraniyawa da suke da dangantaka da addinin muslunci a kasar malazia tare da wasu daga cikin littafn da aka tarjama daga harshen farisanci zuwa harshen Malayu wanda shi ne harshen da ake Magana da shi a hukumance a kasar.
Majiyar tsaron kasar ta sanar cewa 'ya'yan wata kungiyar da ke dauke da makamai ne suka kai hari a jiya a wasu unguwanni da ke gefen birnin Bujumbura, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 4.
Wani jami'in 'yan sanda a birnin ya fadi yau cewa, bisa ga binciken da suka gudanar sun gane cewa 'ya'yan wata sabuwar kungiyar 'yan bindiga ce da ke tsananin adawa da jam'iya mai mulki a kasar suka kai harin, a lokacin da mutane suke kallon wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar turai, da aka buga a daren jiya tsakanin Kungiyoyin kwallon kafa na da kuma Barcelona, lamarin day a yi sanadiyar mutuwar mutane 4 a nan take, wasu kuma suka samu raunuka.
Jami'in ya ce 'yan bindigar sun kai harin ne da bindigogi masu aman wuta a unguwar Nkinga, bayan da suka samu bayanai da ke cewa wasu 'ya'yan jam'iyya mai mulki a kasar suna kai komo a yankin.
835510