Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da wata gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Abu Dabi na kasar hadaddiyar daular larabawa, tare da halartar makaranta da mahardata daga sassan kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa ana shirin fara gudanar da wata gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Abu Dabi na kasar hadaddiyar daular larabawa, tare da halartar makaranta da mahardata daga sassan kasar kamar yadda aka saba gudanarwa akowace shekara kuma cikin wane watan azumin Ramadan.
Wannan dai shi karo na shida da aka fara gudanar da irin wannan gasa tare da halartar wasu daga cikin wakilan cibiyoyin addini na kasar da ma wakilai na ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar, wadda kuma tare da hadin gwiwa da ita da kuma cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta kasar ne aka shirya wannan gasa.
Ana shirin fara gudanar da wata gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Abu Dabi na kasar hadaddiyar daular larabawa, tare da halartar makaranta da mahardata daga sassan kasar wadda take gefen tekun fasha.
835935