Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na msa.mit cewa an fara gudanar shirye-shiryen gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki da akeshirin gudanarwa a birnin Boston na jahar Machost da ke kasar Amurka da ake saran gudanarwa a cikin watan gobe kamar yadda bayanin ya tabbatar.
Kungiyar hadin kan dalabai musulmi da suke karatun jami'a a jahar ne suka shirya gudanar da wannan gasa, da nufin kara karfafa gwiwar junasu kan riko da koyarwar addininsu, da kuma sanin kur'ani da mayar da shi abin koyi bisa la'akari da yanayin kasar da suke rayuwa a cikinta.
Fara gudanar shirye-shiryen gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki da akeshirin gudanarwa a birnin Boston na jahar Machost da ke kasar Amurka da ake saran gudanarwa a cikin watan gobe wanda babbar cibiyar dalibai musulmi ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NN an bayyana cewa, an bude wani babban baje koli na kayayyakin rubuce-rubucen Iraniyawa da suke da dangantaka da addinin muslunci a kasar malazia tare da wasu daga cikin littafn da aka tarjama daga harshen farisanci zuwa harshen Malayu wanda shi ne harshen da ake Magana da shi a hukumance.
836627