Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoto da cewa, a zantawar da ya yi da daya daga cikin manyan jami'an ma'aikatar bunkasa harkokin al'adu da ilimin muslunci ta kasar Iran Muhammad Baqer Khoramshad ya bayyana cewa, bisa la'akari da gagarumin ci gaban da kasar Iran take samu a dukaknin bangarori da kuma rawar da jami'oin kasar suke takawa a wadannan fagage, za a iya cewa kasar tana samun ci gaba ne sakamakon kokarin jami'oin a dukkanin bangarori na ilimi, kasantuwar duk wani ci gaba ya doru ne a kan ilimi.
A bangare guda kuma a wani labarin na daban, Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: mallakar makamin nukiliya ta yi hannun riga da dan-Adamtaka, kuma babban hatsari ne ga kasashen da suka mallake shi.
A ganawar da ya yi da gidan talabijin na Euronews a jiya laraba; shugaban kasar Iran Dr Mahmud Ahmadi Najad ya bayyana cewa: shirin makamashin nukiliyar kasar Iran na zaman lafiya ne tsantsa, kuma babu wani shiri da Iran ke yi domin mallakar makamin nukiliya, sannan kasar Iran tana daga cikin kasashen duniya 'yan kadan da shirin makamashin nukiliyarsu ke gudana karkashin kulawar hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya.
Ahmadi Najad ya kara da cewa; 'yan siyasar kasashen yammacin Turai ne kawai ke zargin cewa kasar Iran na kokarin kera makamin nukiliya, ba masana ilimin kimiyya ba. Kamar yadda shugaban na Iran ya jaddada cewa: mallakar makamin nukiliya ba kawai lamari ne da ya yi hannun riga da dan-Adamtaka ba, wani babban hatsari ga kasashen da suka mallake shi, kamar yadda yake hatsari ga sauran al'ummomi.
836732