Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an habarta cewa, ana kara samun yawan yin amfani tsakanin al’ummar kasar Rahsa, inda ya zuwa yanzu bayanai suka tabbatar da cewa yin amfani da irin wadannan kayayyaki ya kai kashi arbz’in cikin dari a kasar kamar dai yadda bayanan suka tabbatar.
awani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na saphirnews an bayyana cewa, za a rika watsa shirye-shiryen addini daga masallacin kasar Faransa daga birnin Vinio a cikin wani shafin yanar gizo kai tsaye, da suka hada da salloi da karatun kur’ani da kuma wa’azi da ake yi a bayan kammala salloli da sauran harkoki da muslmin kasar suke gudanarwa a kowace shekara adaidai irin wannan lokaci.
An kammala gudanar da wani zaman tattaunawa tsakanin addinai biyu na muslunci da kuma Buda, wanda shi ne karo na biyu da za a gudanar da irinsa abirnin qom da ke jamhuriyar muslunci ta Iran, tare da halartar masana daga dukkanin bangarorin mabiya addinan guda biyu masu dadadden tarihi.
Addinin muslunci da kuma addinin Buda, dukkaninsu addinai da suke da manufa fahimtar juna tsakaninsu da sauran addinai, duk da irin banbancin akida ta addini da ke akwai tsakaninsu, amma sun hadu a kan wasu abubuwa na ‘yan adamtaka, wadanda suke da matukar muhimamnci a rayuwar dan adam ga abki daya.
837716