Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya samu daga shafin sadarwa na yanar gizo na aljazeera an bayyana cewa, dubban daruruwan mutanen kasar Yemen ne suka gudanar da zanga-zangar nuna kyama ga gwamnatin shugaba a saleh a ranar jumar farko ta watan Ramadan mai alfarma a birnin sana fadar mulkin kasar da sauran birane da ke cikin kasar baki daya.
ya nakalto wani rahoto da aka buga a shafin yanatr gizo na jaridar Al-riyad da ake bugawa a kasar saudiyya, da ke cewa daliban makarantun sakandare 500 ne da sukahardace kur’ani mai tsarki za agirmama ayankin Katif da ke gabacin kasar Saudiyya, wanda mafi yawan mazauna cikinsa mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa ne a wannan rana.
Labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an sheda cewa, makarancin kur’ani mai tsarrki Sayyid Sadeq ya samu gagarumar karbuwa agasar karatun kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a kasar Kuwait a matsayi na kasa da kasa, inda ake gudanar da rana ta hudu bayan fara ta ranar juma’ar da ta gabata, inda daruruwan makaranta daga kasashen musulmi da na larabawa suke karawa da juna domin nuna irin baiwar da Allah madaukakin sarki ya yi musu.
837748