IQNA

Dubban Mutane Sun Halarci Sallar Juma’ar Farko Ta Watan Ramadan A Qods

21:11 - August 07, 2011
Lambar Labari: 2166755
Bangaren kasa da kasa, dubban daruruwan palastinawa ne suka halarci sallar juma ta farkon watan ramadan mai alfarma a masallacin Qods dukkuwa da irin matakan da sojojin yahudawan sahyuniya suka dauka na hana musulmi shiga masallacin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoton da ke cewa dubban daruruwan palastinawa ne suka halarci sallar juma ta farkon watan ramadan mai alfarma a masallacin Qods dukkuwa da irin matakan da sojojin yahudawan sahyuniya suka dauka na hana musulmi shiga masallacin domin gudanar da salla.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an fara gudanar da shirin taron nan da aka saba gudanarwa akasar Morocco kan warkokin addinin muslunci, da ke samun halartar mawaka na kasar baki daya a karo na goma sha daya, domin raya dararen watan ramadan mai alfarma a kasar wanda ake gudanarwa bisa kulawar ma’aikatar harkokin addini.
Kotun kasar Birtaniya ta yanke hukunci dauri kwanaki saba’in a kan wani jami’in tsaron kasar da ya wulakanta kur’ani mai tsarki, da nufin hakan ya zama darasi ga masu hankoron tsokanar mabiya addinin muslunci a kasar ta hanyar wulaknata abubuwansu masu tsarki, kamar yadda wasu suka dauki irin wannan salo a wasu kasashen nahiyar turai.
Shi dai wannan sojin kasar Birtaniya mai suna Andro Rayan ya sace wani kwafin kur’ani mai tsarki daga wani dakin karatu, inda ya tafi da shi a gaban mutane ya kone shi da wuta, kotun ta ce bisa laifi da aka samu Anro da aikatawa ta yanke masa hukuncin daurin kwanaki saba’in a gidan kaso.
kotun kasar Birtaniya ta yanke hukunci dauri kwanaki saba’in a kan wani jami’in tsaron kasar da ya wulakanta kur’ani mai tsarki, da nufin hakan ya zama darasi ga masu hankoron tsokanar mabiya addinin muslunci a kasar ta hanayar wulaknata abubuwansu masu tsarki.
837885



captcha