Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya samu wani rahoto a shafin yanar gizo da ke cewa, wasu na ta hankoron ganin sun fassara zanga-zangar da ake guadanarwa ta kyamar gwamnatin zalunci da fir’ananci ta bahrain da cewa ‘yanadawa ne ‘yan shia kawai alhali ba haka lamarin yake ba domin kuwa, akwai ‘yan sunna da ma wadanda ba musulmi ba, da kuma kungiyoyin kare hakkin dan adama da suka hada kowane bangare a cikin masu zanga-zanga.
labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na allafrica cewa, ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Algeria na shirin kafa wata cibiya ta bincike kan tasirin azumi ta fuskacin kiwon lafiya, wanda likitoci da dma da suka gudanar da bincike sun tabbatar da cewa azumi na da babban tasiri ta fuskacin kara lafiya ga mai azumi da kuma yadda yake bayar da lafiya.
wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lorientlejour an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman tattaunawa a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon, dangane da hanyoyin habbaka ttatalin arzikin kasashen muslumi da kuma yadda zai yi tasiri a cikin harkokin tattalin arziki na duniya, ba tare da fuskantar wasu matsaloli ba.
A bangare guda kuma an fara gudanar da taron baje koli na kayan fasahar masana a musulunci a kasar Birtaniyam, wanda babbar cibiyar kula da kayan tarihin muslunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa tun daga makon da ya gabata a babban dakin tarukanta da ke birnin London fadar mulkin kasar.
Taron yana samun halartar masana kan harkokin al’adu da tarihi daga jami’ar birnin London da kuma wasu cibiyoyi na mabiya addinin muslunci da ke cikin sassan kasar, haka nan kuma ana nuna wasu daga cikin abubuwan da aka samar na fasahar musulunci a kasar weadanda suke nuna kokarin masana musulmi masu fasaha da suke gudanar da ayyuka.
837941