IQNA

Yawaita Bayani A Tarjama Na Nisantar Da Mai Karatu Ko Saurare Daga Ma'ana

15:28 - August 08, 2011
Lambar Labari: 2167331
Bangaren kasa da kasa, rubuta Karin haske da bayani a cikin tarjamar kur'ani mai tsarki idan hakan ya yi yawa sosai yana janye hankali mai karatu ko saurare daga hakikanin ma'anar abin da ayar take yin ishara zuwa gare shi.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ya gudanar tare da daya daga cikin masu ayyukan tarjamar kur'ani mai tsarki a kasar India a babbar jami'ar muslunci ta kasar ya bayyana cewa, rubuta Karin haske da bayani a cikin tarjamar kur'ani mai tsarki idan hakan ya yi yawa sosai yana janye hankali mai karatu ko saurare daga hakikanin ma'anar abin da ayar take yin ishara zuwa gare shi a farkon bahasi.

Lauyan mutumin nan da ake zargi da kai mummunan harin ta'addancin da aka kai kasar Norway a jiya ya bayyana cewar mutumin da ake zargin mai suna Anders Behring Brevik ya amince da cewa shi ne ya kai wannan hari da ya yi sanadiyyar mutuwar alal akalla mutane 92 da raunana wasu da dama.
Mr. Geir Lippestad lauyan mutumin da ake zargin ya shaidawa gidan talabijin din NRK na kasar Norway din cewa wanda ake zargin ya amince da aikata wannan danyen aikin, yana mai cewa duk da cewa abin da ya aikata din mummunan abu ne amma dai ya zama wajibi ya aikata hakan. Har ila yau lauyan ya kara da cewa tun a shekara ta 2009 ya ke shirya kai wannan harin.
Wasu bayanai da aka watsa a shafin internet suna nuni da cewa shi dai wannan mutumin yana da rikau ne da kuma kiyayya ga musulmi kamar yadda bayanai suke ci gaba da fitowa dangane da irin shirin da ya yi na kai wannan harin.
Yan sanda dai sun ce nan gaba kadan za a gurfanar da wannan mutumin a gaban kotu da zargin da ayyukan ta'addanci guda biyu. Na farko dangane da mutuwar mutane bakwai sakamakon tashin tashin bomb a garin Oslo, na biyu kuma dangane da kashe mutane sama da tamanin da biyar da ake zargin ya bindige su a wani sansanin matasa, kusa da birnin Oslon.
838624


captcha