Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam an bayyana cewa, daya daga cikin masu fafutuka a Bahrain Karim Mahrus ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Saudiyya ita ce babban karfen kafa ga yunkurin da al'ummar kasar Bahrain suke yin a neman 'yanci da sauyi daga mulkin fir'aunanci da kama karya na gidan sarautar Bahrain da ke samun goyon bayan kasashen yammacin turai da yahudawa.
Gungun 'yan siyasar Bahrain bangaren adawa na Alwifaq ya sanar da janyewa baki daya daga tattaunawar da sarkin kasar ya kira, sakamakon rashin karba abubuwan da al'ummar kasar Bahrain suke bukata.
Daya daga cikin jagororin gungun 'yan siyasar na Alwifaq Hadi Musawi ya bayyana cewa, sun dauki wannan matakin ne bayan da suka fahimci cewa tattaunawar ta yi kama da wasan kwakwayo, domin kuwa ana tattauna abin da sarki da gwamnatin kasar suke bukata ne, ba abin da al'ummar Bahrain ke bukata ba, domin kuwa a cewarsa sun shiga tattaunawar ne suna masu riko da sauye-sauyen da al'ummar kasar fatan gani a cikin harkokin siyasa da mulkin kasar.
Da dama daga cikin matasan kasar Bahrain da suke gudanar da zanga-zangar neman sauyi, sun yi Allawadai da wannan tattaunawa, wadda ake gudanarwa a lokacin mahukuntan kasar suke ci gaba da kame daruruwan masu zanga-zanga tare da azabtar da su, inda wasunsu sukan rasa rayukansu sakamakon azabtarwa. 838517