IQNA

Al'ummar Kasar Bahrain Za Su Ci Gaba Da Zanga-Zangar Neman Sauyi

10:38 - August 09, 2011
Lambar Labari: 2167666
Bangaren kasa da kasa, al'ummar kasar Bahrain za su ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman sauyi a cikin dukaknin harkokin siyasa da mulki a kasar duk kuwa da irin matakan rashin imani da jami'an tsaron masarautar Alikhalifa ke dauka kansu.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na tashar talabijin din alalam an bayyana cewa, al'ummar kasar Bahrain za su ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman sauyi a cikin dukaknin harkokin siyasa da mulki a kasar duk kuwa da irin matakan rashin imani da jami'an tsaron masarautar Alikhalifa ke dauka kansu na kisan gilla da dauri da makamantan haka.

A zantawar da ta hada shi da gidan talabijin din an Al-alam daya daga cikin masu fafutuka a kasar Bahrain Karim Mahrus ya bayyana cewa, a daidai lokacin da mahukuntan kasar Bahrain suke raya cewa suna bukatar tattaunawa tare da bangaren adawa, suna ci gaba da kame duk wanda ya nuna rashin gamsuwa da salon mulkinsu.

Ya kara da cewa da babu gudu bau ja da baya, domin kuwa al'ummar kasar Bahrain za su ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman sauyi a cikin dukaknin harkokin siyasa da mulki a kasar duk kuwa da irin matakan rashin imani da jami'an tsaron masarautar Alikhalifa ke dauka kansu na danniya tare da taimakon munafukan daulolin larabawa.

839261

captcha