IQNA

Kiyaye Dabi'u Na Kur'ani A Cikin Aikin Jarida Babban Wajibi Ne

14:50 - August 09, 2011
Lambar Labari: 2167916
Bangaren kasa dasa, babban sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci ta duniya ya kirayi masu gudanar da aikin jarida da su kiyaye muhimamn abubuwa na kyawawan dabi'u da kur'ani mai tsarki ya koyar dad an adam a cikin rayuwa.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labar da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, Ayatollah Taskhiri babban sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci ta duniya ya kirayi masu gudanar da aikin jarida da su kiyaye muhimamn abubuwa na kyawawan dabi'u da kur'ani mai tsarki ya koyar dad an adam a cikin rayuwa ta zamantakewa.

Ya ci gaba da cewa a kowane lokaci ana bukatar mutum a cikin dukkanin ayyukansa ya kiyae abin da Allah madaukakin sarki ya yi umurni da shi, domin kuwa dan jarida wani mutum ne da mutane suke kallonsu tamkar wakilinsu a cikin dukkanin abubuwan da suke faruwa aduniya, kuma abin day a fada shi ne ma'ani wajen gane gaskiyar lamari.

Ayatollah Taskhiri, wanda shi ne babban sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci ta duniya ya kirayi masu gudanar da aikin jarida da su kiyaye muhimamn abubuwa na kyawawan dabi'u da kur'ani mai tsarki ya koyar da dan adam a cikin rayuwarsa ta yau da kullamu, kamar yadda ya zo a cikin nassosi.

839500


captcha