Bangaren kasa da kasa, an buga tare da yada wani littafi mai suna yunkurin Imam Hussain (AS) a cikin harshen turancin Ingilishi a birnin karbala na kasar Iraki, wanda ake ganin cewa yin hakan yana da kyau.
Kmafanin dllancin labaran kur'ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NUN an bayyana cewa, an buga tare da yada wani littafi mai suna yunkurin Imam Hussain (AS) a cikin harshen turancin Ingilishi a birnin karbala na kasar Iraki da nufin kara fadada fahimtar iyalan gidan manzon Allah a cikin al'ummar musulmi, ta yadda hakan zai taimaka masu fahimtar wannan harshe.
Imam Hussain (AS) jikan manzon Allah ya taka gagarumar rawa wajen rike ragamar jagorancin addinin muslunci bayan shahadar Imam Hassan (AS) a hannun azzaluman sarakunan bani umayya, inda zuriyar manzon Allah ta shiga cikin wani halin na kunci da zalunci da takura domin kawai a kawar da al'umma daga shiriyar manzo.
Buga tare da yada wani littafi mai suna yunkurin Imam Hussain (AS) a cikin harshen turancin Ingilishi a birnin karbala na kasar Iraki, wanda ake ganin cewa yin hakan yana da kyau na da matukar muhimmanci a cikin wannan zamani da muke rayuwa a cikinsa.
839563