IQNA

A Daren Yau Ne Za Bude Bangaren Kasa Da Kasa Na Baje Kolin Kur'ani

14:08 - August 10, 2011
Lambar Labari: 2168547
Bangaren kasa da kasa, a daren yau ne za a bude bangaren kasa da kasa na kasuwar baje kolin kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Tehran tare da halartar malamin addini kuma shugaban majalisar kusanto da mazhabobin musulunci.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labar da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, Ayatollah Taskhiri babban sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci ta duniya ya kirayi masu gudanar da aikin jarida da su kiyaye muhimamn abubuwa na kyawawan dabi'u da kur'ani mai tsarki ya koyar dad an adam a cikin rayuwa ta zamantakewa.
Ya ci gaba da cewa a kowane lokaci ana bukatar mutum a cikin dukkanin ayyukansa ya kiyae abin da Allah madaukakin sarki ya yi umurni da shi, domin kuwa dan jarida wani mutum ne da mutane suke kallonsu tamkar wakilinsu a cikin dukkanin abubuwan da suke faruwa aduniya, kuma abin day a fada shi ne ma'ani wajen gane gaskiyar lamari.
Hojjatol islam Muhamad Hamidi, wanda shi ne babban sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci ta duniya ya kirayi masu gudanar da aikin jarida da su kiyaye muhimamn abubuwa na kyawawan dabi'u da kur'ani mai tsarki ya koyar da dan adam a cikin rayuwarsa ta yau da kullamu, kamar yadda ya zo a cikin nassosi.
840550
captcha