Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labar da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na observer an bayyana cewa, Daga cikin abubuwan da musulmunci ya kebanta da su shi ne saukakawa, a duk lokacin da wani hukunci ya zama da wahala to Allah madaukakin sarki ya kan saukaka ma muminai saba ma umurnin Allah da aikata zunubi da yin ha’inci da zalunci yana cutar da mu ne kai tsaye, ba Allah madaukakin sarki ba.
Addinin muslunci bai hana mabiyansa jin dadi ba, amma dai ya saka tsari a cikin dukkanin komai, ta yadda mabiyansa ba za su fita daga dokokin ubangiji ba, Mutum ba shi da hujjar aikata sabon ubangiji alhali Allah ya hore masa hanyoyin da zai bi domin samun sa’ada ta duniya da lahira.
Kusantar sabo na gab da ya zama aikata shi, domin kuwa sai mutum ya kusanci sabo ne zuciyarsa tare da zugar shedan zai kai ga aikata sabon, shi ya sanya a wasu wurare kur’ani ke yin hani da kusantar sabo domin kada mu fada cikin laifin aikata shi.
Dukkanin abubuwan da aka shata na ka’idoji da doki na azumin watan ramadan, babbar manufar hakan ita ce samun tsarkakar ruhi da taqawa, da kuma nisantar sabon ubangiji.
840509