IQNA

An Nuna Wani Kwafin Kur'ani Mai Tsarki Da Aka Danganta Da Imam Ali (AS)

10:34 - August 11, 2011
Lambar Labari: 2168869
Bangaren kasa da kasa, an nuna wani kwafin kur'ani kur'ani mai tsarki da aka danganta shi da Imam Ali (AS) a taron baje koli na kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a karo na goma sha biyar, wanda ke samun halartar dubban mutane.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa an bayar da rahoton wata tattaunawa tare da Alireza Isma'ili, wanda ya ce an nuna wani kwafin kur'ani kur'ani mai tsarki da aka danganta shi da Imam Ali (AS) a taron baje koli na kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a karo na goma sha biyar, wanda ke samun halartar dubban mutane daga cikin gida da kuma kasashe ketare.

Daga cikin ka’idoji da dokoki na azumi addinin muslunci ya gindaya wa musulmi a cikin watan ramadan, a lokacin azumi haramun ne su kusanci matayensu, kamar yadda haramun ne su ci abinci ko abin sha, har sai bayan shan ruwa, amma kafin safkar wannan ayar kusantar mataye ya kasance cikin abubuwan da aka hana a cikin watan ramadan baki daya har ma cikin dararensa, lamarin da ya yi wa wasu daga cikin musulmi matukar wahala.

Inda suka fadi wannan jarabawa ta ubangiji, amma daga bisani Allah ya safkar da wannan aya kuma ya yi musu afuwa kan hakan, kuma ka halasta musu kusantar mataye a daga bayan shan ruwa har zuwa kafin fitowar alfijir, koda yake wannan hukunci ya takaitu ne ga wadanda ba suna cikin i’itikafi ne ba ne a masallaci, domin su hakan bai halasta gare su ba.

Wannan aya mai albarka ta siffanta mata a matsayin tufa ga maza, kamar yadda mazaje suke a matsayin tufa ga matayensu, tofa bisa ga al’ada tana rufe tsiraici da aibi, tana kuma kawata wanda ya saka ta. A kan haka ne kur’ani ya bayar da wannan misali, domin kuwa ma’aurata suna matsayin tufa ne ga junansu, kowanne dayansu yana taimaka dayan ne, yana yi masa nasiha, yana nuna masa gaskiya, ya shiryear da shi zuwa ga abin da Allah ke so domin ya aikata, da nusar da shi abin da Allah ba ya so domin kaurace masa, sakamakon kaunar juna da tusayi da ke tsakaninsu.

840747
captcha