IQNA

Ayatollah Taskhiri Babban Bako A Baje Kolin Kur'ani Bangaren Waje

12:36 - August 11, 2011
Lambar Labari: 2168895
Bangaren zamantakewa, babban bako a baje kolin kur'ani mai tsarki a bangaren kasashen ketare da aka bude a daren jiya, babban sakatare cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci ta duniya Ayatollah Taskhiri shi bako na musamman a wurin.


Kamfanin dilalncin labara iqna ya habarta cewa, Ayatollah Tskhiri babban bako a baje kolin kur'ani mai tsarki a bangaren kasashen ketare da aka bude a daren jiya, babban sakatare cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci ta duniya shi bako na musamman a wurin inda ya gabatar da jawabi ga mahalarta taron, wani abu da musulunci ya shahara da shi, shi ne tsari a cikin dukkanin lamurra, da suka hada da hukunce-hukuncensa da sauran lamurran na zamantakewar mabiyansa.

Misali, loktan salla an sanya su zama daga lokacin fitowar alfijir, ko gushewar rana, ko faduwarta da dai makamantan hakan, azumi na wajibi daga farkon watan ramadan zuwa karshensa, tare da yinsa a daga fitowar alfijir zuwa bayan faduwar rana, lokacin aikin haji a cikin wata na musamman wato zul hijja, tare da ka’idoji da hanyoyi na musamman da ake yinsa.

Dangane da batun ganin wata ma musulunci yama ka’idoji da ake yin la’akari da su, ta yadda za su dace da yanayi na kwanan wata na shekara a kowane lokaci da cikin lokuta, lamarin da yake ba musulmi damar sanin takamai lokutan da za su gudanar da ayyukan ibadarsu kamar yadda Alah ya yi umurni.

Abu na biyu shi ne batun aikin hajji, akwai ayyukan da wasu daga cikin musullmi suke yi wadanda ada kafin musulunci suke yi a lokacin da suke zuwa Ka’aba, a lokacin musulunci ma suna yin wadannan ayyukan a lokacin aiki haji, sai aka bayyana musu hakan da cewa surkulle ne na jahiliyya da ba shi da wuri a cikin addinin muslunci. 840663
captcha